Tsohon mataimakin shuaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ƙoƙarin kauce wa alhakin matsin tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke fuskanta, bayan shugaban ya zargi ’yan adawa da haddasa yunwa da talauci a ƙasar.
A cikin wata sanarwa da Phrank Shaibu, daraktan yaɗa labarai na kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku a jam’iyyar ADC, ya fitar, Atiku ya kwatanta kalaman Tinubu da mutumin da ya kunna wuta sannan ya zargi maƙwabtansa da hayaƙin da ta haifar.
Atiku ya bayyana cewa jam’iyyar APC ta shafe shekaru takwas tana mulkin Najeriya kafin Tinubu ya hau karagar mulki, sannan gwamnatin Tinubu ta ƙara kusan shekaru uku da rabi a kan mulki.
Saboda haka, ya ce bai kamata gwamnati ta ɗora wa ’yan adawa alhakin matsin rayuwa da ake fuskanta ba.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi tambayoyi kan manufofin gwamnatin Tinubu, ciki har da cire tallafin man fetur, faduwar darajar naira, ƙaruwar talauci da matsalolin tsaro da suka haɗa da kashe-kashe, garkuwa da mutane da kuma korar al’umma daga muhallansu.
Haka kuma, Atiku ya buƙaci a yi bayani kan wasu kuɗaɗen gwamnati da ya ce suna buƙatar ƙarin haske, ciki har da kashe-kashen da suka shafi tsaron makamashi da ayyukan bututun mai na kamfanin NNPC.
Ya ce ya kamata a auna nasarar gwamnati bisa yanayin rayuwar ’yan Najeriya, maimakon bayanan da take gabatarwa a tarukan siyasa.
Atiku ya kuma bayyana zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 a matsayin damar da ’yan Najeriya za su tantance ayyukan gwamnatin Tinubu ta hanyar ƙuri’unsu.