An kauce wa hatsarin jirgin sama a Abuja ranar Alhamis, bayan ƙofar wani jirgin haya mai zaman kansa mallakin kamfanin Triton Aviation ta faɗo jim kaɗan bayan tashinsa daga filin jirgin Nnamdi Azikiwe.
Jirgin mai lamba T7-SEI yana kan hanyarsa daga Abuja zuwa Legas lokacin da lamarin ya faru. Hakan ya tilasta wa matuƙan jirgin ayyana dokar ta-ɓaci tare da neman taimakon gaggawa.
Bayan haka, masu kula da zirga-zirgar jiragen sama sun umurci jirgin ya koma Abuja domin saukar gaggawa, yayin da jami’an kashe gobara da ma’aikatan lafiya suka shiga shirin ko-ta-kwana.
Rahoton ya nuna cewa jirgin ya sauka lafiya da misalin ƙarfe 4:34 na yamma agogon UTC, mintuna 14 bayan kiran gaggawar. Daga bisani, jami’an filin jirgin suka tabbatar da cewa ƙofar ta ɓace daga jikin jirgin.
A wani bidiyo da ya yaɗu, wasu manoma sun ce sun gano ƙofar a wata gona da ke Abuja. Hukumar NSIB ta tabbatar da faruwar lamarin tare da tura masu bincike domin gano musabbabinsa, yayin da ba a tabbatar da adadin fasinjojin da ke cikin jirgin ba.