Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fitar da jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar gwamnan Jihar Gombe a zaɓen da za a gudanar ranar 6 ga Fabrairu, 2027, ba tare da sunan tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ba.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa INEC ta amince da ’yan takara 16 domin fafatawa a zaɓen, ciki har da Jamilu Isyaku Gwamna na APC, Bala Bello Tinka na ADC da Babayo Ardo Kumo na NDC.
Pantami, wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na PDP bayan ficewa daga APC, ya kasance cikin jerin sunayen da INEC ta fitar a ranar 29 ga Agusta, amma sunansa bai bayyana a sabon jerin da aka fitar ranar Asabar ba.
Tun da farko, Ahmed Mailantarki ya ƙalubalanci nasarar Pantami a kotu, lamarin da ya sa Babbar Kotun Tarayya da ke Gombe ta soke zaɓen fidda gwanin farko tare da umartar PDP ta sake gudanar da shi. Pantami ya sake samun nasara a zaɓen na biyu.
Sai dai har yanzu INEC ba ta bayyana dalilin cire sunan Pantami daga jerin ƙarshe na ’yan takarar ba.