Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce za ta fitar da jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar gwamna da na majalisun dokokin jihohi da za su fafata a zaɓen shekarar 2027 a ranar Asabar, 10 ga Oktoba, 2026.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa jam’iyyun siyasa 21 daga cikin 22 da aka yi wa rajista ne suka gabatar da ’yan takara 936 na gwamna da mataimakan gwamna a jihohi 28 na ƙasar.
Haka kuma, ya ce an gabatar da ’yan takara 9,692 domin neman kujerun majalisun dokokin jihohi a faɗin Najeriya.
Za a gudanar da zaɓen gwamna a jihohi 28 a ranar 6 ga Fabrairu, 2027, yayin da zaɓen majalisun dokokin jihohi zai gudana a dukkan jihohin ƙasar, ban da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
A cewar tanadin sashe na 32(1) na Dokar Zaɓe ta 2026, INEC za ta wallafa cikakkun sunaye da adireshin ’yan takarar da aka amince da su a ofisoshinta da kuma shafinta na intanet, aƙalla kwanaki 60 kafin ranar zaɓe.
Sashe na 32(2) na dokar ya kuma tanadi cewa jam’iyyar siyasa da ta gano an cire sunan ɗan takararta daga jerin da aka wallafa za ta iya sanar da hukumar a rubuce cikin kwanaki 14, tare da sa hannun shugaban jam’iyyar na ƙasa da sakatarenta da kuma takardar rantsuwa.
Wa’adin sauya sunayen ’yan takara ya ƙare ranar 19 ga Satumba, 2026, yayin da wa’adin miƙa fom ɗin tsayawa takara ya ƙare ranar 26 ga Satumba, 2026.