Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiAn saki ‘yan NYSC 20 da aka yi garkuwa da su a...

An saki ‘yan NYSC 20 da aka yi garkuwa da su a Imo

‘Yan Najeriya 20 da ke shirin fara yi wa ƙasa hidimar NYSC, tare da wani mutum guda da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Owerri-Onitsha a Jihar Imo, sun samu ‘yancin.

‘Yan Najeriya 20 da ke shirin fara yi wa ƙasa hidimar NYSC, tare da wani mutum guda da aka yi garkuwa da su a kan hanyar Owerri-Onitsha a Jihar Imo, sun samu ‘yancin.

An ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su ne daga dajin Amakohia-Ubi da ke ƙaramar hukumar Owerri West, biyo bayan wani samame na haɗin gwiwa da hukumomin tsaro suka gudanar.

A yanzu haka an kai su asibitin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da ke Owerri, inda suke samun kulawar lafiya tare da gudanar da gwaje-gwajen da suka dace.

Daraktan Janar na Hukumar NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu, yana asibitin DSS da ke Owerri, inda yake magana da waɗanda aka ceto.

Yana tare da Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Imo, Daraktan DSS da Kwamandan Brigade na 34 Artillery da ke jihar.

Har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan yadda aka gudanar da aikin ceton ba, ciki har da ko an kama wasu daga cikin masu garkuwar ko kuma an biya kuɗin fansa.

Sai dai a wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, Ani Iniedu, ya fitar, rundunar ta ce:

“Ana ci gaba da ƙoƙarin kama waɗanda ke da hannu wajen satar mutanen, yayin da ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro ke ci gaba da gudanar da ayyukan haɗin gwiwa domin gurfanar da duk waɗanda ke da hannu a gaban ƙuliya.”

An yi garkuwa da waɗanda lamarin ya rutsa da su ne a ranar 1 ga Oktoba, yayin da suke tafiya daga Ibadan ta Jihar Oyo zuwa sansanonin horar da ‘yan NYSC da ke jihohin Abia da Akwa Ibom.

Motoci biyu da ke ɗauke da waɗanda za su yi hidimar ƙasa sun fuskanci hari ne kusa da Umunoha a ƙaramar hukumar Mbaitoli ta Jihar Imo.

Bayan sace su, hukumomin tsaro sun ƙaddamar da aikin haɗin gwiwa na bincike da ceto domin gano waɗanda aka sace da kuma masu garkuwa da su.

Daga baya rundunar ‘yan sandan Jihar Imo ta ce jami’anta sun gano sansanin masu garkuwar ta hanyar amfani da jirgi mara matuƙi, amma ba su iya shiga wurin nan take ba saboda rahotannin cewa an dasa abubuwan fashewa na IED a yankin.

Daga bisani ‘yan sanda suka ƙara tura kayan aiki na musamman, ciki har da buldoza da motocin sulke, domin ƙara ƙaimi wajen kai wa waɗanda aka yi garkuwa da su ɗauki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments