Mazauna garin Bindin da wasu garuruwan da ke makwabtaka da shi a ƙaramar hukumar Maru ta Jihar Zamfara sun gudanar da zanga-zanga kan rahoton janye jami’an soji daga yankin, bayan jerin hare-haren ƴan bindiga da suka yi sanadin asarar rayuka.
Wani manazarci kan harkokin tsaro, Bakatsine, ne ya wallafa bayanin a shafinsa na X.
Dubban mazauna yankin, ciki har da mata, sun fito kan tituna ranar Laraba tare da tare ayarin motocin sojoji domin hana su barin yankin.
Zanga-zangar ta biyo bayan hare-haren da ake zargin yan ta’addan wani fitaccen ɗan bindiga mai suna Kachalla Gwaska Dankarami suka kai a Bindin da Gobirawar Chali.
A cewarsa, mazauna yankin sun ce hare-haren sun yi sanadin mutuwar jami’an tsaro da fararen hula da dama, yayin da sama da mutane 10,000 suka bar gidajensu domin neman mafaka a wuraren da suka fi tsaro.
Masu zanga-zangar sun ce ci gaba da kasancewar sojoji a yankin na da matuƙar muhimmanci ga tsaronsu, inda suka bayyana fargabar cewa janye dakaru zai bar al’ummomin cikin sauƙin fuskantar wasu hare-haren.
Wani mazaunin yankin ya roƙi hukumomi da su sauya shawarar da aka bayar na janye sojojin.
“Idan sojoji suka tafi, wa zai kare mu? Tuni muke rayuwa cikin tsoro bayan abin da ya faru,” in ji shi.
Rahotanni sun ce masu zanga-zangar sun dage cewa ayarin sojojin ya ci gaba da kasancewa a yankin, suna gargadin cewa ficewar dakaru na iya haifar da gibin tsaro wanda ƴan bindiga za su iya amfani da shi wajen kai hare-hare ga wasu al’ummomi.