Yusuf Abdullahi Itas, ɗan Majalisar Dokokin Jihar Bauchi mai wakiltar mazabar Itas/Gadau, ya janye daga takarar neman sake komawa majalisar a zaɓen 2027.
Itas, wanda ke neman sake tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar APM, ya sanar da matakin nasa ne a wata wasiƙa mai kwanan wata 5 ga Oktoba, 2026, wadda ya aikewa shugaban jam’iyyar na jihar.
A cikin wasiƙar mai taken, “Janye takara daga neman kujerar mazabar Itas/Gadau a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi,” ɗan majalisar ya sanar da jam’iyyar a hukumance cewa ba zai sake neman kujerar a zaɓen 2027 ba.
Ya bayyana cewa matakin nasa “na kashin kai ne. “
Yayin da yake godiya ga shugabannin APM da mambobinta bisa damar da suka ba shi ta wakiltar jam’iyyar, Itas ya kuma nuna godiyarsa ga al’ummar mazabarsa bisa ƙarfafawa da goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake kan mulki.
Janyewarsa daga takarar ya zo ne kasa da makonni uku bayan bulaliyar Majalisar Dokokin Bauchi, Musa Wakili Nakwada, shi ma ya sanar da cewa ba zai tsaya takara a zaɓen 2027 ba.