Fitacciyar jarumar Kannywood, Fati Muhammad, ta bayyana irin wahalhalun da ta ce ta fuskanta sakamakon goyon bayanta ga Atiku Abubakar.
Fati ta ce, “Dalilin Atiku aka kona min gidana, dalilin Atiku aka kona min motata,” tana mai bayyana irin abubuwan da ta ce sun faru da ita saboda matsayarta na siyasa.
Jarumar ta kuma ce saboda abubuwan da suka faru, ta hakura da zaman Kaduna, inda ta dawo Kano domin ci gaba da rayuwarta.
A cewarta, wasu daga cikin mutanen da take ganin masoyanta ne sun juya mata baya saboda matsayar da ta dauka kan Atiku da siyasar da take yi.
Fati ta ce, “Ni na sha wuya da Atiku a lokacin da ku ba ku kaunarsa,” tana bayyana cewa ta kasance cikin masu goyon bayan Atiku tun lokacin da wasu ba sa nuna masa irin wannan goyon baya.