Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiLabaraiTawagar kasar Benin ta koka kan yadda aka mu’amalance su a wasan...

Tawagar kasar Benin ta koka kan yadda aka mu’amalance su a wasan bankwanan Messi – Rahoto

Rahotanni sun ce tawagar ƙasar Benin ta nuna rashin jin daɗi kan yadda aka gudanar da wasu abubuwa bayan wasan sada zumunta da ta fafata da Argentina, wanda Lionel Messi ya buga.

Rahotanni sun ce tawagar ƙasar Benin ta nuna rashin jin daɗi kan yadda aka gudanar da wasu abubuwa bayan wasan sada zumunta da ta fafata da Argentina, wanda Lionel Messi ya buga.

A cewar rahoton, Benin ba ta samu wani ƙarin kuɗin alawus ko kari ba bayan wasan, sannan kuma ba a ba ta wani kaso daga cikin kuɗaɗen da aka samu daga taron ba.

Rahoton ya kuma ce babu musayar riguna tsakanin ’yan wasan Benin da Argentina, yayin da ’yan wasan Benin ba su samu damar daukar hotuna tare da ’yan wasan Argentina ba.

Haka kuma, an ce ba a ba tawagar Benin damar shiga ɗakin sauya kaya na Argentina ba bayan kammala wasan.

Rahoton, wanda ɗan jaridar bincike Romain Molina ya wallafa, ya ce tawagar Benin ta nuna rashin jin daɗi kan yadda aka mu’amalance su yayin taron. Sai dai ba a gabatar da wata sanarwa kai tsaye daga hukumar ƙwallon ƙafa ta Benin da ke tabbatar da dukkan waɗannan zarge-zargen ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments