Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamna Abba Kabir Yusuf ya gana da babban wakilin sarkin Kano na...

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gana da babban wakilin sarkin Kano na 15

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gudanar da wata ganawar sirri da Alhaji Aminu Babba Dan’agundi, Sarkin Dawaki Babba kuma babban mai ba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, shawara an Abuja.

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gudanar da wata ganawar sirri da Alhaji Aminu Babba Dan’agundi, Sarkin Dawaki Babba kuma babban mai ba Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, shawara an Abuja.

Ganawar ta gudana ne a masaukin jihar Kano da ke Abuja, inda ganawar ta dauki kusan sa’o’i biyu, kamar yadda wata majiya mai masaniya kan lamarin ta bayyana.

Majiyar ta ce Dan’agundi ya isa gidan gwamnatin ne bayan gayyatar da Gwamna Yusuf ya yi masa, kafin su shiga ganawar sirri. Sai dai ba a bayyana abubuwan da suka tattauna ba.

Ganawar ta zo ne a lokacin da ake samun sabbin abubuwa a rikicin masarautar Kano, musamman bayan rahotannin cewa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya hau doki duk da takunkumin da aka sanya kan hawan doki da jerin gwanon gargajiya.

A baya, Dan’agundi ya ce bangaren Aminu Ado Bayero na jiran ganin matakin da gwamnatin jihar za ta dauka, yayin da Kotun Koli ta dage sauraron shari’ar rikicin masarautar Kano zuwa watan Afrilu 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments