Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Kaduna ta jingine yanke hukunci kan ƙarar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya shigar yana ƙalubalantar matakin Babbar Kotun Jihar Kaduna na hana bayar da belinsa.
El-Rufa’i ya garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara ne domin neman a sake duba hukuncin da Babbar Kotun Jihar Kaduna ta yanke kan buƙatarsa ta neman beli.
Kotun ta saurari hujjojin ɓangarorin da abin ya shafa kafin ta ɗage yanke hukunci zuwa wata rana da za a sanar nan gaba.
Har yanzu dai ba a bayyana ranar da kotun za ta dawo domin yanke hukunci kan ƙarar ba.