Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaShekarau: Buhari ne ya fara cire tallafin man fetur kafin Tinubu

Shekarau: Buhari ne ya fara cire tallafin man fetur kafin Tinubu

Tsohon Gwamnan Kano, tsohon Sanata kuma tsohon Ministan Ilimi, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce matakan kawo ƙarshen tallafin man fetur sun fara ne tun lokacin gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, kafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau kan mulki.

Shekarau ya ce Tinubu ya san cewa an riga an ɗauki matakan kawo ƙarshen tsarin tallafin, shi ya sa a ranar 29 ga Mayun 2023, lokacin da ya hau kan karagar mulki, ya bayyana cewa tallafin man fetur ya ƙare, da kalaman “Subsidy is gone.”

A cewar Shekarau, gwamnatin Buhari ta riga ta fara ɗaukar matakan da suka shafi kawo ƙarshen biyan tallafin kafin mika mulki ga gwamnatin Tinubu.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su tambayi gwamnonin jihohinsu game da yadda tsarin tallafin man fetur yake a lokacin gwamnatin Buhari da kuma matakan da aka ɗauka kafin sauyin gwamnati.

Shekarau ya bayyana wannan matsaya ne yayin da yake magana kan batun cire tallafin man fetur da kuma yadda aka tafiyar da tsarin kafin da bayan sauyin gwamnati a shekarar 2023.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments