Jam’iyyar APC ta ce kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, na shirin tattara kuri’u miliyan 50 domin sake zaɓar shugabannin biyu a zaɓen 2027.
Jam’iyyar ta ce Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, za ta jagoranci wani babban taron mata a Abuja, wanda ake sa ran zai haɗa sama da mata 20,000 daga sassa daban-daban na Najeriya.
Taron zai haɗa shugabannin mata, ’yan kasuwa, ƙwararru da masu shirya ayyukan al’umma, inda za a tattauna manufofin gwamnatin Tinubu da kuma hanyoyin isar da saƙon jam’iyyar ga al’umma gabanin zaɓen 2027.
Mamba a kwamitin wayar da kan mata na APC, Gimbiya Gloria Akobundu, ta ce za a gabatar da wasu shirye-shiryen gwamnatin tarayya da take cewa sun taimaka wa ’yan Najeriya.
Daga cikin shirye-shiryen da ta ambata akwai Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND), shirin CREDICORP, ayyukan more rayuwa, tallafin kuɗi kai tsaye da wasu shirye-shiryen tallafa wa marasa galihu.
Akobundu ta ce NELFUND ya samu rajistar ɗalibai sama da miliyan 1.4, yayin da adadin buƙatun lamuni ya haura miliyan 1.69.
Ta kuma ce an raba sama da Naira biliyan 191 ta cibiyoyin ilimi sama da 320 domin taimaka wa ɗalibai wajen biyan kuɗin karatu.
Dangane da ayyukan more rayuwa, ta ce gwamnatin tarayya ta kammala sama da kilomita 2,700 na manyan tituna, yayin da wasu ayyukan hanyoyi da layin dogo ke ci gaba a sassa daban-daban na ƙasar.
Haka kuma, ta bayyana CREDICORP a matsayin wani shiri da ke bai wa ’yan Najeriya damar samun lamuni domin wasu bukatu, ciki har da ilimi, gyaran gidaje da samar da makamashi mai sabuntawa.
APC ta ce mata za su taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al’umma kan manufofin gwamnatin Tinubu tare da isar da saƙon jam’iyyar zuwa matakai daban-daban kafin zaɓen 2027.