Aƙalla mutane biyar ne suka mutu, yayin da wasu shida suka ɓace bayan wani jirgin ruwa ya kife a mashigar Buruku da ke Kogin Benue, a ƙaramar hukumar Buruku ta jihar Benue.
Jirgin katakon na ɗauke da fasinjojin da ke dawowa daga jana’iza ne lokacin da ya kife da misalin ƙarfe 11 na safiyar Asabar.
Shaidu sun ce sama da mutane 120 ne aka ceto bayan hatsarin, yayin da aka fara bayyana cewa mutane 11 sun ɓace. Ya zuwa yammacin Lahadi, an gano gawarwaki biyar, yayin da ake ci gaba da neman sauran shida.
Jami’in hulɗa da jama’a na Tombo Maritime Workers Union, Saai Oryina, ya ce biyar ɗin da aka gano sun fito ne daga yankin Mbayion na ƙaramar hukumar Gboko.
Ya ce rashin amfani da rigunan kariya na daga cikin abubuwan da ke ƙara haɗarin mutuwa a irin wannan hatsari, inda ya bukaci fasinjoji da su riƙa amfani da su.
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Benue, SEMA, ta tura jami’anta wurin domin gudanar da bincike da taimakawa wajen aikin ceto.
A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Benue ta dakatar da reshen ƙungiyar ma’aikatan ruwa na Buruku, tare da dakatar da ma’aikacin da ke kula da layin, sannan ta bayar da umarnin kama kyaftin ɗin jirgin.
Gwamnatin ta kuma umarci a tabbatar da amfani da rigunan kariya a dukkan mashigai na ruwa, tare da bai wa mai wani jirgin ruwa da aka bari a wurin wa’adin kwanaki bakwai ya cire shi, ko gwamnati ta ƙwace shi.