Sunday, October 18, 2026
HomeLabaraiAn hallaka mutane biyu yayin harin Lakurawa a Sokoto

An hallaka mutane biyu yayin harin Lakurawa a Sokoto

Akalla mutane biyu, ciki har da wani ɗan banga, sun mutu yayin da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa sun kai hari ƙauyen Ungushi da ke ƙaramar hukumar Kebbe ta Jihar Sokoto.

Akalla mutane biyu, ciki har da wani ɗan banga, sun mutu yayin da ake zargin ’yan ta’addan Lakurawa sun kai hari ƙauyen Ungushi da ke ƙaramar hukumar Kebbe ta Jihar Sokoto.

Mazauna yankin sun ce ’yan ta’addan sun farmaki ƙauyen ne da yammacin Lahadi tare da buɗe wuta, lamarin da ya tilasta ’yan banga shiga artabu da su na sama da awa guda.

Wani jami’in tsaron al’umma ya ce an tura sojoji, ’yan sanda da sauran jami’an tsaro zuwa yankin bayan samun labarin harin, amma maharan sun riga sun tsere.

Ya ce ɗaya daga cikin wadanda aka kashe manomi ne da ke dawowa daga gona, yayin da ɗayan ɗan banga ne. Wani mutum kuma ya samu raunin harbin bindiga, inda aka garzaya da shi asibiti.

An kuma samu rahoton cewa an kashe wasu daga cikin maharan yayin musayar wuta, sai dai ba a samu damar tabbatar da wannan bayanin da kansa ba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar da faruwar harin, amma ya ce yana jiran ƙarin bayani daga jami’in ’yan sanda na yankin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments