Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce matakan tattalin arziki masu tsauri da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka sun taimaka wajen kare Najeriya daga faɗawa cikin babbar matsalar tattalin arziki.
Shettima ya amince cewa ’yan Najeriya na fuskantar tsadar rayuwa da matsaloli sakamakon sauye-sauyen da ake aiwatarwa, amma ya ce matakan sun zama dole domin gyara tare da daidaita tattalin arzikin ƙasar.
Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na ɗaukar wasu matakai domin rage wa ’yan kasa radadin sauye-sauyen, tare da samar da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar jama’a.
Daga cikin shirye-shiryen da ya ambata akwai shirin samar da motocin lantarki, wanda gwamnati ke ganin zai taimaka wajen rage kudin sufuri.
Haka kuma, Shettima ya yi magana kan shirin bayar da tallafin lamunin karatu ta hannun NELFUND, wanda aka samar domin taimaka wa ɗalibai wajen biyan kudaden karatu da ci gaba da karatunsu.
Mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada cewa gwamnatin Tinubu na ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen da take ganin za su samar da ingantaccen tattalin arziki mai ɗorewa a Najeriya.