Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasa2027: Tsohon ɗan majalisa ya roƙi Atiku da Obi su marawa Tinubu...

2027: Tsohon ɗan majalisa ya roƙi Atiku da Obi su marawa Tinubu baya

Tsohon ɗan majalisar dokokin Jihar Legas, Hon. Jude Idimogu, ya yi kira ga tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party, Peter Obi, da su janye daga takarar shugaban ƙasa a 2027 domin marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya.

Idimogu ya ce gwamnatin Tinubu na bukatar karin lokaci domin kammala sauye-sauyen da take aiwatarwa, yana mai cewa wa’adin shekaru huɗu kaɗai ba zai isa a cimma dukkan manufofin gwamnatin ba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ga manema labarai, tsohon ɗan majalisar ya bayyana cewa ya yi imani da manufofin Tinubu da kuma shirin gwamnatin na Renewed Hope, inda ya bukaci ’yan Najeriya su ci gaba da ba shugaban ƙasar goyon baya da addu’a.

Idimogu ya yi kira na musamman ga Atiku Abubakar da ya janye daga takarar 2027, yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar da Tinubu sun dade da sanin juna kuma suna da tarihin siyasa tare.

Ya ce ya kamata Atiku ya jira har zuwa shekarar 2031, sannan ya nemi kujerar shugaban ƙasa, maimakon kalubalantar Tinubu a zaɓen 2027.

Haka kuma, Idimogu ya bukaci Peter Obi da ya mara wa Tinubu baya, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen haɗin kan yankin Kudu.

A cewarsa, idan manyan ‘yan siyasar Kudu suka rarrabu a zaben 2027, hakan na iya bai wa ‘yan siyasar Arewa damar samun shugabancin ƙasar.

Ya bayyana Peter Obi a matsayin mutum mai mutunci kuma ɗan’uwa, amma ya ce a wannan lokaci ya kamata ya goyi bayan Tinubu domin tabbatar da haɗin kan Kudu.

Idimogu ya kare manufofin Tinubu

Tsohon ɗan majalisar ya kuma kare manufofin gwamnatin Tinubu, yana mai cewa sauye-sauyen tattalin arziki da sauran matakan da gwamnatin ke dauka na bukatar lokaci kafin talakawa su fara ganin cikakken amfaninsu.

Ya ce ba za a iya gina kasa cikin rana ɗaya ba, yana mai cewa Tinubu ya shafe sama da shekaru uku yana mulki kuma yana bukatar karin lokaci domin kammala wasu daga cikin manufofinsa.

Idimogu ya bayyana cewa har yanzu yana da yakinin cewa Tinubu na da kwarewar jagorantar Najeriya, tare da yin kira ga ‘yan kasa daga sassa daban-daban da su mara wa gwamnatin baya.

A cewarsa, ya yi imanin cewa jam’iyyar APC na da damar samun nasara a zaben shugaban ƙasa na 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments