Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar (ADC), Rotimi Amaechi, ya ce zai janye daga tikitin Atiku Abubakar tare da yi wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kamfe idan farashin litar man fetur ya sauka zuwa N600.
Amaechi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Politics Today na Channels Television a ranar Juma’a, inda ya soki gwamnatin Tinubu kan hauhawar farashin sufuri da tsadar rayuwa.
Ya ce idan farashin fetur ya koma N600 kan kowace lita, zai je gidan mai da kansa domin tabbatar da farashin, sannan ya cika alkawarin da ya dauka na janye daga matsayin mataimakin Atiku tare da mara wa Tinubu baya a zaɓen 2027.
Amaechi ya ce: “Idan fetur ya sauka zuwa N600 gobe, zan janye daga matsayin mataimakin shugaban ƙasa na Atiku, sannan in yi wa Shugaba Tinubu kamfe.”
Ya kuma kalubalanci gwamnatin tarayya kan tasirin manufofinta na tattalin arziki, musamman game da rage farashin sufuri da sauƙaƙa matsin rayuwa ga ’yan Najeriya.
A yayin hirar, Amaechi ya kuma bayyana tsadar rayuwa da farashin sufuri a matsayin wasu daga cikin manyan batutuwan da ke tasiri ga rayuwar ’yan Najeriya a halin yanzu.
Jam’iyyar ADC ta sanar da Amaechi a matsayin mataimakin Atiku Abubakar a tikitin jam’iyyar na zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a watan Yunin 2026.