Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiKano: An kama mutane biyar kan zargin lalata fastocin Tinubu da Abba

Kano: An kama mutane biyar kan zargin lalata fastocin Tinubu da Abba

Rundunar ’yan sandan Kano ta ce ta kama wasu mutane biyar bisa zargin hannu wajen lalata fastoci da allunan tallace-tallacen Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu ’yan siyasa a jihar.

Kwamishinan ’yan sandan Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai kan matakan tsaro da dokar da ta haramta hawan dawakai a bainar jama’a a Kano.

Bakori ya bayyana cewa an cafke waɗanda ake zargin ne bayan gudanar da bincike kan lalata kadarori a lokacin da ake samun tashin hankali da ya shafi hawan dawakai da jerin gwanon jama’a.

A cewarsa, rundunar ta kammala binciken mutanen da aka kama tare da gurfanar da su a gaban kotu. Ya kuma tabbatar da cewa ’yan sanda za su ci gaba da ɗaukar matakin doka kan duk wanda aka samu da hannu wajen aikata laifukan da ka iya kawo cikas ga zaman lafiya.

Kamen ya zo ne bayan wata fitowar da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero, ya gudanar a ranar Lahadi.

Kwamishinan ya ce rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin mutanen da suka raka Sarkin sun lalata fastoci da allunan tallace-tallacen Tinubu, Gwamna Abba Kabir Yusuf da wasu ’yan siyasa, lamarin da ya ƙara haifar da tashin hankali a daidai lokacin da ake ci gaba da samun rikici kan masarautar Kano.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments