Amurka ta tura ƙarin kusan sojoji 9,000 zuwa Gabas ta Tsakiya, a wani mataki da ya ƙara yawan kasancewar sojojin ruwan ƙasar a yankin yayin da ake ci gaba da samun ƙaruwar tashin hankali tsakaninta da Iran.
Rahoton Associated Press ya ce ƙarin sojojin na tafiya ne a cikin wasu jiragen ruwa da suka haɗa da jirgin yaƙi na USS Theodore Roosevelt da rundunar jiragen ruwa ta USS Makin Island. Jiragen na ɗauke da sama da jami’an ruwa 7,000 da sojojin Marine kusan 2,000.
A cewar wani jami’in Amurka da ya yi magana ba tare da bayyana sunansa ba saboda batun ya shafi ayyukan soji masu muhimmanci, zuwan waɗannan jiragen na iya sa Amurka ta kasance da manyan jiragen yaƙi guda uku a Gabas ta Tsakiya zuwa ƙarshen watan Oktoba.
A halin yanzu, jiragen USS George H.W. Bush da USS George Washington suna yankin, tare da rundunar USS Boxer. Idan sabon rundunar ta isa, adadin sojojin ruwa da Marines na Amurka a yankin zai iya wuce 20,000, baya ga ɗaruruwan jiragen sama.
Matakin na zuwa ne yayin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake bayyana cewa akwai yiwuwar Amurka ta ɗauki matakin soji kan Iran. Trump ya ce zai iya ƙara kai hare-hare bayan zaɓen tsakiyar wa’adin Amurka na ranar 3 ga Nuwamba, kodayake ya ce ba zai bayyana cikakken shirin sojinsa ba.
Rahotanni sun ce wannan ƙarin sojoji ya ƙara yawan ƙarfin sojin ruwan Amurka a yankin, yayin da ake ci gaba da samun takaddama kan makomar rikicin Amurka da Iran da kuma yunƙurin diflomasiyya na rage tashin hankalin.
Sai dai, rahotannin da suka fito sun bayyana cewa wasu daga cikin bayanan da suka shafi ayyukan sojin Amurka na nan gaba ba a tabbatar da su a hukumance ba, saboda wasu bayanan na cikin sirrin ayyukan soja.