Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kashe manoma 15 a yankunan Ala da Musune da ke ƙaramar hukumar Marte a Jihar Borno.
Rahotanni sun ce maharan sun yi wa manoman kwanton bauna ne a gonakinsu a yammacin ranar Laraba, yayin da suke gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Majiyoyi sun bayyana cewa mutane 18 ne suka je yankin, inda aka gano gawarwakin mutum 15 daga cikinsu.
An binne waɗanda aka kashe a ranar Alhamis bisa tsarin addinin Musulunci, yayin da har yanzu ba a san inda sauran mutane uku suke ba.
Jami’in hulɗa da jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar harin, yana mai cewa jami’an tsaro na ci gaba da ƙoƙarin gano inda mutanen uku da suka bace suke.
Majiyoyin yankin sun ce waɗanda lamarin ya rutsa da su sun haɗa da manoma da masu tara itacen girki, ciki har da matasa, dattawa da maza masu iyalai.
Wata majiya ta ce maharan sun kai wa mutanen hari ne ba zato ba tsammani, inda suka kashe su. Wasu daga cikin waɗanda aka kashe kuma sun samu munanan raunuka.
Kungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da kisan, tana mai bayyana harin a matsayin mummunan cin zarafin fararen hula.
Kungiyar ta buƙaci hukumomin Najeriya da su ɗauki matakan gaggawa domin kare al’ummomin da ke zaune a yankunan da ke fuskantar barazanar hare-haren ’yan ta’adda.