Saturday, October 17, 2026
HomeTsaroTinubu ya yi wa yan Najeriya albishir kan kawo karshen matsalar tsaro

Tinubu ya yi wa yan Najeriya albishir kan kawo karshen matsalar tsaro

Tinubu ya bayyana shirin Gwamnatin sa na kawo karshen matsalar tsaro.

A yayin da ake ci gaba da fuskantar matsalolin rashin tsaro a sassa daban-daban na Najeriya wanda hakan ke tayar da hankulan jama’a Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kawo karshen matsalar.

Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a jihar Legas, ranar Litinin, 15 ga watan Disamban 2025 yayin da ya bude taron shekara-shekara na babban hafsan sojojin kasa na 2025.

Tinubu ya bayyana shirin da gwamnatinsa ke yi domin cewa kwanciyar hankali ya dawo zukatan ‘yan Najeriya

Shugaba Tinubu ya nuna cewa gwamnatinsa za ta hada dukkan kayan aikin sojoji da hukumomin tsaro domin murkushe barazanar tsaro da kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa a fadin Najeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments