Gwamnatin Tarayya da Amurka sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da nufin ƙara zuba jarin Amurka a fannin ma’adinai na Najeriya tare da bunƙasa albarkatun ma’adinan ƙasar.
Ministan Ma’adinai da Bunƙasa Ma’adinai na Najeriya, Dele Alake, da Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Christopher Landau, ne suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a Ofishin Jakadancin Najeriya da ke New York ranar Laraba.
An rattaba hannun ne a yayin taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.
Alake ya sanar da yarjejeniyar a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis, inda ya ce tsarin yarjejeniyar zai ƙunshi bayanan ƙasa da binciken ma’adinai, haɓaka da sarrafa ma’adinai, samar da ababen more rayuwa da ƙarfafa ƙwarewar fasaha.
A cewar Alake, gwamnatin Najeriya ta kiyasta darajar albarkatun ma’adinan ƙasar da kusan Dala biliyan 700.
Alake ya ce:
“Wannan wani muhimmin mataki ne wajen ƙarfafa haɗin gwiwar Najeriya da Amurka kan albarkatun ma’adinanmu, waɗanda darajarsu ta kai kusan dala biliyan 700. Tsarin ya ƙunshi bayanan ƙasa da binciken ma’adinai, haɓaka da sarrafa ma’adinai, ababen more rayuwa da ƙwarewar fasaha.
“Najeriya ba za ta ci gaba da kasancewa ƙasar da ake kwashe ɗanyen kayan amfanin ƙasa daga cikinta ba, yayin da wasu ke amfana da su. Muna son a ƙara sarrafa ma’adinai a cikin gida, samar da ingantattun ayyukan yi, ƙarfafa ƙwarewa da kuma faɗaɗa damar kasuwancin ‘yan Najeriya.
Yarjejeniyar ta zo ne yayin da gwamnatin tarayya ke ƙara ƙoƙarin jawo jarin ƙasashen waje zuwa fannin ma’adinai tare da ƙara sarrafa albarkatun ma’adinan Najeriya a cikin gida domin ƙara musu daraja.