Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSojoji sun karrama jami’ai huɗu da suka yi ritaya a Kaduna

Sojoji sun karrama jami’ai huɗu da suka yi ritaya a Kaduna

Rundunar Sojojin Najeriya ta yaba wa sadaukarwar jami'an ga tsaron ƙasa

Rundunar Sojojin Najeriya ta 1 ta karrama jami’ai huɗu da suka yi ritaya a wani taron bankwana da aka gudanar a zauren taro na rundunar da ke jihar Kaduna.

A wani saƙo da rundunar ta wallafa a shafinta na X ranar Alhamis, ta ce an an shirya shi taron ne a ranar Laraba domin girmama jami’an bisa shekarun da suka shafe suna yi wa ƙasa.

Babban Kwamandan sashe na 1 kuma Kwamandan JTF Operation Fansan Yamma shiyya ta 1, Manjo Janar Abubakar Wase, ne ya jagoranci taron.

Da yake jawabi a wajen taron, Wase ya yaba wa jami’an da suka yi ritayar bisa jajircewarsu da kuma gagarumar gudunmawar da suka bayar ga rundunar sojojin Najeriya.

A cewar Babban Kwamandan, wannan mataki ya nuna al’adar rundunar ta wajen nuna godiya ga jami’an da suka yi wa ƙasa hidima yadda ya kamata.

Ya kuma tabbatar musu cewa za su ci gaba da kasancewa cikin Rundunar Sojojin Najeriya, tare da kira gare su da su ci gaba da hulɗa da al’ummar sojoji tare da kiyaye kyawawan matakan ladabtarwa da suka gada a lokacin hidimarsu.

Jami’an da aka karrama sun haɗa da Master Warrant Officer (MWO) Ladi Mustapha na Hedikwatar 1 Division; MWO Oche Sunday, Babban Magatakarda na Hedikwatar 1 Division; Warrant Officer Obile Mu’azu na Hedikwatar 1 Division; da Mista Oyagha Theophilus na sashen kuɗi na 1 Division.

Da yake magana a madadin sauran jami’an da suka yi ritaya, MWO Oche Sunday ya nuna godiyarsa ga Babban Kwamandan da shugabancin 1 Division bisa damar da suka ba su ta yi wa ƙasa hidima.

Ya gode wa rundunar bisa jagoranci, horarwa da kuma ƙarfafa gwiwa ba tare da gajiyawa ba da suka samu a tsawon lokacin da suka yi suna aiki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments