Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiGwamnan Sokoto ya kafa kwamiti don tantance sabbin ma’aikata

Gwamnan Sokoto ya kafa kwamiti don tantance sabbin ma’aikata

Kwamiti zai tantance sabbin ma’aikata 3,100 tare da tabbatar da biyan albashinsu.

Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya amince da kafa wani kwamiti da zai tantance tare da sauƙaƙa biyan albashin sabbin ma’aikatan gwamnati 3,100 da aka ɗauka aiki a jihar.

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na gidan gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce Shugaban Ma’aikatan Jihar Sokoto, Abdulkadir Ahmad, ne zai jagoranci kwamitin, yayin da Babban Mataimaki na Musamman kan Harkokin Shari’a da Gudanarwa, Gandi Umar Muhammad, zai kasance mataimakin shugaban kwamitin.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da wakilai daga Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnati, Babban Akanta Janar na Jihar, Babban Akanta Janar na Ƙananan Hukumomi, Hukumar Kula da Malamai ta Jihar, da Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC).

Haka kuma, Abdulmajid Sidi daga Ma’aikatar Kuɗi da Shehu Abdullahi, Daraktan Gudanarwa da Ayyukan Gabaɗaya, na cikin mambobin kwamitin. Junaidu U. Junaidu, Mataimakin Babban Akanta Janar, zai kasance sakataren kwamitin.

An ɗora wa kwamitin alhakin tabbatar da cewa ma’aikatan da aka tura zuwa ma’aikatu, hukumomi da sassan gwamnati daban-daban sun halarci wuraren aikinsu.

Haka kuma, kwamitin zai tabbatar da cewa an fara biyan albashin ma’aikatan da suka cika sharuddan tare da fara aiki yadda ya kamata cikin gaggawa.

Ana sa ran kwamitin zai gabatar da rahotonsa ga gwamnatin jihar cikin makonni huɗu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments