Rundunar sojin Najeriya ta ceto mutane bakwai da aka yi garkuwa da su, ciki har da ɗalibai mata shida na Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA), a jihar Katsina.
Rundunar Operation FANSAN YAMMA ta ceto mutanen ne a kan hanyar Daye zuwa Malumfashi, ƙaramar hukumar Danmusa, bayan da aka samu kiran gaggawa cewa ‘yan bindiga sun kai hari kan motar haya da ke tafiya daga Kaduna zuwa Katsina.
Dakarun sun isa wurin cikin gaggawa, lamarin da ya tilasta maharan tserewa tare da barin waɗanda suka yi garkuwa da su. Mutanen da aka ceto sun haɗa da ɗalibai mata shida da direban motar.
Rundunar ta ce an ceto su lafiya, sannan aka gudanar musu da binciken tsaro da duba lafiyarsu kafin miƙa su ga jami’an da za su mayar da su ga iyalansu da hukumomin jami’ar.