Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce a kusan shekaru 40 da ya shafe yana siyasa, bai taɓa ganin shugaban Najeriya da ya samar da tsare-tsaren farfaɗo da ƙasar kamar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.
Masari ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyo da aka wallafa a Facebook, yayin da yake jawabi ga wasu mata a wani taro da aka ce an gudanar a Kaduna.
Ya kuma soki masu sukar gwamnatin Tinubu da cewa ba ta yi wani abu ba, yana mai cewa irin wannan suka ya taɓa kasancewa a lokacin gwamnatocin tsoffin shugabannin Najeriya, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.
Sai dai kalaman na Masari na nuna ra’ayinsa ne kan yadda yake kallon tsare-tsaren gwamnatin Tinubu, yayin da ake ci gaba da samun muhawara kan tasirin manufofin gwamnatin da halin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki.