Fadar Shugaban Ƙasa ta ƙalubalanci ɗan takarar jam’iyyar NDC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027, Peter Obi, da ya cika alkawarin da ya yi na janyewa daga takarar, bayan gwamnatin Jihar Anambra ta musanta ikirarin da ya yi cewa ya bar jihar ba tare da wani bashin kuɗi ko wata takarda ta bashi da ba a biya ba.
Mai ba Shugaban Ƙasa Bola Tinubu shawara na musamman kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya yi wannan ƙalubalen a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba, inda ya ambaci sabbin bayanan da gwamnatin Anambra ta gabatar kan basussuka da kuma wasu kuɗaɗen da aka bari ba a biya ba lokacin mulkin Obi.
“Peter Obi ya yi ikirarin cewa ya bar Anambra ba tare da wani bashi ba,” Onanuga ya rubuta, inda ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta kawo hujjoji da alkaluma kan bashin da ya shafi ma’aikatan Hukumar Ruwa, malamai, fansho da kuma alawus-alawus na ritaya.
Ya kuma ce gwamnatin Obi ta ciwo wasu basussuka domin abubuwa marasa muhimmanci a lokacin da yake gwamnan jihar, tare da tambayar ko tsohon gwamnan zai cika barazanar da ya yi a baya ta janyewa daga takarar shugaban ƙasa idan aka tabbatar da cewa ikirarinsa ba gaskiya ba ne.
Rikicin ya fara ne bayan Kwamishinan Yaɗa Labarai da Gyaran Hali na Jihar Anambra, Dr Law Mefor, ya fitar da wata sanarwa yana musanta ikirarin Obi cewa gwamnatinsa ta bar jihar ba tare da wasu basussuka ko nauyin kuɗi da ba a biya ba.
Mefor ya ce gwamnatin Gwamna Chukwuma Soludo ta biya kusan Naira biliyan 22 na bashin alawus-alawus na ritaya da gwamnatocin baya suka bari.
Ya ce bashin ya shafi tsofaffin ma’aikatan gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi da kuma malamai.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Obi ta bar wasu basussukan rance da kuma bashin albashi, fansho da alawus-alawus na ritaya, waɗanda gwamnatocin da suka biyo bayanta suka gada.
A cewar gwamnatin jihar, akwai basussukan rance guda takwas daga ƙasashen waje da aka danganta da ayyukan da gwamnatin Obi ta aiwatar ko kuma ta gada. Gwamnatin ta ce ragowar bashin ya kai Dala miliyan 92.35, wanda ya yi daidai da Naira biliyan 127.37 a ranar 30 ga Yunin 2026.
An ce an karɓi waɗannan rance ne domin ayyukan yaƙi da zazzabin cizon sauro, dakile zaizayar ƙasa, kiwon lafiya, ilimi, bunƙasa al’umma da kuma ci gaban harkar noma.