Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Atiku Abubakar, ya karɓi bakuncin Aisha Buhari, matar marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, a gidansa da ke Abuja ranar Laraba.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya bayyana ziyarar Aisha Buhari a matsayin mai muhimmanci.
Atiku bai bayyana dalilin ziyarar tsohuwar uwargidan shugaban ƙasar ba, amma ya ce ziyarar ta tunatar da duk masu son ganin an samu ingantacciyar Najeriya cewa ya kamata a sanya jin daɗin jama’a, mutuncinsu da makomarsu a gaba.
“Yau na yi farin cikin karɓar bakuncin tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa, H.E. Aisha Buhari,” in ji Atiku.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce a sassa daban-daban na Najeriya, iyalai da dama na fuskantar matsin rayuwa sakamakon tashin farashin abinci, sufuri, ilimi, kiwon lafiya da sauran muhimman abubuwan buƙata.
Ya ce ’yan Najeriya sun cancanci samun tattalin arzikin da zai bai wa masu aiki tuƙuru damar samun sakamako, tare da dawo da damammaki da ba jama’a damar rayuwa cikin mutunci.
“Wannan ita ce Najeriya da ya kamata mu gina tare, ƙasa wadda za ta sake aiki domin amfanin jama’arta,” in ji shi.