Dan wasan gaba na ƙungiyar Barcelona, Lamine Yamal, ya bayyana cewa ya yi imanin ya cancanci lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2026, sakamakon nasarorin da ya samu tare da ƙungiyarsa da kuma tawagar ƙasarsa.
Yamal mai shekara 19 ya ce shi da tauraron Real Madrid, Kylian Mbappé, su ne daga cikin fitattun ’yan wasa biyu mafi ƙwarewa a duniya a halin yanzu.
A wata hira da aka yi da shi, Yamal ya bayyana cewa nasarar lashe kofin LaLiga tare da Barcelona da kuma kofin duniya tare da tawagar Spain sun ƙara masa ƙarfin gwiwar cewa ya cancanci babbar kyautar kwallon kafa ta duniya.
Dan wasan ya ce yana ganin nasarorin da ya samu a bana sun ba shi damar fafatawa sosai da Mbappé wajen neman kyautar Ballon d’Or ta 2026.