Rundunar Sojojin Najeriya ta ce dakarun Bataliya ta Musamman ta 7, ƙarƙashin Sashe na Biyu na Operation FANSAN YAMMA, sun fatattaki ’yan ta’adda daga wani sansani da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza a Jihar Sokoto.
Rundunar ta ce yayin samamen, dakarun sun kwato bindigar kirar PKT, bindigogin AK-47, harsasai da kuma babura da ake zargin ’yan ta’addan ke amfani da su.
Majiyoyin soji sun bayyana cewa dakarun sun kutsa cikin wasu wuraren da aka gano akwai barazanar ’yan ta’adda, ciki har da ƙauyukan Manu, Alkasim da Kandam, da kuma dajin Magarya, bayan samun bayanan sirri kan ayyukan ’yan bindigar a yankin.
Rahotanni sun ce dakarun sun yi arangama da ’yan ta’addan a dajin Magarya, inda suka buɗe musu wuta, lamarin da ya tilasta wa ’yan ta’addan barin sansaninsu tare da tserewa cikin daji.
Bayan arangamar, dakarun sun ci gaba da bincike a yankin da kewaye, inda suka gano makamai, harsasai da wasu kayayyakin da ake zargin ’yan ta’addan ke amfani da su.
Rundunar ta ce samamen na daga cikin ci gaba da ayyukan soji da ake gudanarwa domin tarwatsa maboyar ’yan ta’adda, daƙile zirga-zirgarsu tare da dawo da zaman lafiya da tsaro ga al’ummomin Arewa maso Yammacin Najeriya.