Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajePutin ya tattauna da wakilan Amurka kan kawo ƙarshen yaƙin Ukraine

Putin ya tattauna da wakilan Amurka kan kawo ƙarshen yaƙin Ukraine

Fadar Kremlin ta ce Shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya gudanar da abin da ta bayyana a matsayin tattaunawa mai cike da gaskiya da wakilan Amurka kan hanyoyin kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.

Mai taimaka wa Putin, Yuri Ushakov, ya ce wakilan Amurka sun gabatar da wasu shawarwari kan yadda za a cimma matsaya tare da kawo ƙarshen yaƙin cikin gaggawa.

Ushakov ya bayyana tattaunawar a matsayin mai ma’ana, cike da gaskiya da fahimtar juna, yana mai cewa ɓangaren Rasha na da kwarin gwiwar cimma manufofin da ya sanya a gaba.

A nasa ɓangaren, jami’in Rasha Kirill Dmitriev, wanda ya halarci tattaunawar, ya bayyana ziyarar wakilan Shugaba Donald Trump, Steve Witkoff da Jared Kushner, a matsayin muhimmiyar ziyara da ke da nufin neman hanyar samar da zaman lafiya.

Tattaunawar na zuwa ne yayin da ake ci gaba da neman hanyoyin da za su taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin da ke tsakanin Rasha da Ukraine.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments