Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan rahoton yadda aka gudanar da shirin tallafin rage radadi ga ’yan Najeriya, inda ya ce akwai buƙatar yin cikakken bincike kan yadda aka raba kuɗaɗen.
Atiku ya ce zai kafa tawagar ƙwararru masu zaman kansu domin nazarin yadda aka kashe Naira biliyan 33.75 da gwamnatin tarayya ta ce ta raba wa gidaje miliyan 3.29 a ƙarƙashin shirin tallafin rage radadi.
Ya bayyana hakan ne ta bakin babban mataimakinsa na musamman kan hulɗa da jama’a, Phrank Shaibu.
A cewarsa, alkaluman da ke cikin rahoton sun haifar da tambayoyi kan yadda tallafin ya kai ga waɗanda aka tanada, musamman talakawan da ke fama da tsadar rayuwa.
Atiku ya yi nuni da cewa idan aka raba Naira biliyan 33.75 tsakanin gidaje miliyan 3.29, kowane gida zai samu kusan Naira 10,258, wanda ya ce ya sa ake buƙatar ƙarin bayani kan yadda aka gudanar da shirin.
Ya kuma ce akwai sabani tsakanin wasu bayanan da gwamnati ta fitar kan adadin kuɗaɗen da aka ware da kuma yawan gidajen da suka amfana.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya yaba wa Ofishin Babban Auditor-Janar na Tarayya kan fitar da rahoton, yana mai cewa gaskiya da riƙon amana suna da muhimmanci wajen gudanar da kuɗaɗen jama’a.
Atiku ya ce tawagar ƙwararrun da zai kafa za ta duba bayanan waɗanda suka amfana, hanyoyin biyan kuɗaɗen, bayanan daidaita lissafi da sauran tambayoyin da suka shafi binciken kuɗaɗen.
Ya ce bayan kammala binciken, za a bayyana sakamakonsa ga ’yan Najeriya domin ƙarin fahimta kan yadda aka gudanar da shirin tallafin.