Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNijar ta zargi Faransa da kitsa yunkurin juyin mulki

Nijar ta zargi Faransa da kitsa yunkurin juyin mulki

Gwamnatin Nijar ta zargi Faransa da hannu wajen goyon bayan wani yunkurin hargitsa kasar da ta ce an yi a ranakun 28 da 29 ga watan Agusta.

A wata sanarwa, hukumomin Nijar sun ce arangamar da ta faru a sansanin sojin sama na 101 da ke Yamai na da alaka da wasu kasashen duniya.

Gwamnatin ta ce ta tattara “kwararan shaidu masu yawa” kan harin, inda ta bayyana cewa tana nazarin yiwuwar kai karar lamarin gaban kotunan kasa da kasa.

Sanarwar ta kuma zargi Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, da jagorantar wasu mutane da kungiyoyi da ake zargin suna goyon bayan yunkurin.

Bugu da kari, Nijar ta yi zargin cewa wasu kasashen Afirka da ba ta bayyana sunayensu ba sun taka rawa wajen lamarin.

Sai dai har yanzu gwamnatin Nijar ba ta gabatar da shaidun da za su tabbatar da wadannan zarge-zarge ba.

Sansanin sojin sama na 101 da aka kai wa hari a ranar 29 ga watan Agusta, yana cikin filin jirgin saman Diori Hamani da ke Yamai.

Sansanin na dauke da jiragen yakin sojin Nijar da jirage marasa matuka, baya ga wata rundunar yaki da ta’addanci ta kasashen Sahel.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments