Kwamishinan Matasa, Wasanni da Yaki da Talauci na Jihar Borno, Saina Buba, ya janye kalaman da ya yi na barazanar yanke yatsan duk wanda ya nuna yatsa ga jami’an gwamnati.
A farkon makon nan, Buba ya yi kalaman ne a wani shirin tallafa wa matasa na City Boy Movement a Maiduguri, inda ya kuma ce masu goyon bayan APC za su samu “zuma”, yayin da wadanda suka ƙi goyon bayan jam’iyyar za su fuskanci bulala.
Kalaman sun jawo suka daga ƙungiyoyin fararen hula da masu sharhi kan siyasa, inda suka ce barazanar daga jami’in gwamnati na iya kawo barazana ga dimokuraɗiyya da ‘yancin faɗar albarkacin baki. Daga bisani, Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta ce ta fara binciken kalaman Buba da wasu shugabannin APC biyu.
Mai magana da yawun rundunar, Anietie Iniedu, ya ce tsokanar jama’a musamman kan batun zaɓe laifi ne a ƙarƙashin doka, yana mai cewa ‘yan sanda sun ɗauki batun da muhimmanci.
Bayan wannan bayani na ‘yan sanda, Buba ya fitar da sanarwa inda ya nuna nadama tare da ba al’ummar Borno da sauran jama’a cikakkiyar uzuri. Ya ce kalamansa ba su da nufin tauye ‘yancin kowa na zaɓe da shiga ƙungiyoyin siyasa.
Kwamishinan ya janye kalamansa a hukumance, yana mai cewa ba su wakiltar manufofin APC ko gwamnatin Gwamna Babagana Zulum ba. Ya ce gwamnatin jihar tana mutunta ‘yancin al’umma tare da bin tsarin dimokuraɗiyya.