Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta tura jami’ai 250 da suka kammala horo zuwa ƙananan hukumomin da ke kan iyakokin jihar, domin ƙarfafa tsaro da inganta martanin jami’an ga matsalolin tsaro da kiran neman agaji.
Jami’an sun kammala horo na tsawon wata guda kan dabarun yaƙi da sarrafa makamai, wanda aka gudanar a sansanonin ’Yan Sandan Mobile Force na 9 da ke Hotoro da kuma 52 da ke Challawa.
Da yake jawabi a wajen bikin yaye jami’an, Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya ce tura jami’an na daga cikin matakan da rundunar ke ɗauka domin ƙarfafa tsaro a kan iyakokin jihar da sauran wuraren da ake fuskantar barazanar tsaro.
Bakori ya umurci jami’an da su kasance masu lura da al’amura, kwarewa da bin dokokin aiki, tare da yin amfani da makamai yadda doka ta tanada da kuma mutunta haƙƙin jama’a.
Ya bayyana cewa jami’an sun samu horo kan dabarun yaƙi, sarrafa bindigogi, tattara bayanan sirri, gano abubuwan fashewa, amfani da ƙarfin da ya dace, kare haƙƙin ɗan Adam, da kuma dabarun aikin ’yan sanda tare da haɗin gwiwar al’umma.
Kwamishinan ya ce rundunar za ta ci gaba da gudanar da ƙarin horaswa na cikin gida domin tabbatar da cewa jami’anta na da ƙwarewa da kayan aikin da suka dace wajen gudanar da ayyukan tsaro.
Bayan kammala bikin, Kwamishinan ya umarci jami’an 250 da su gaggauta zuwa wuraren da aka tura su domin fara aiki.
Ya ce matakin zai taimaka wajen ƙara tsaron iyakokin Kano, ƙara ganin jami’an tsaro a muhimman wurare, da kuma inganta saurin martanin rundunar ga duk wata barazana ta tsaro.