Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaZa a kammala dukkanin ayyukan Tinubu a Abuja kafin 2027 - Wike

Za a kammala dukkanin ayyukan Tinubu a Abuja kafin 2027 – Wike

Ministan Abuja ya kalubalanci masu suka su kwatanta ayyukan Tinubu da na gwamnatocin baya

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya ce za a kammala dukkan ayyukan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta fara a Abuja kafin wa’adin mulkin gwamnatin ya kare.

Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a Fatakwal, Jihar Rivers, inda ya kuma ce babu wata gwamnatin FCT da ta taba samun irin nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu a Abuja.

“Kafin wa’adin wannan gwamnati ya kare, za a kammala duk wani aiki da Bola Tinubu ya fara.” in ji Wike.

Ministan ya kalubalanci masu sukar ayyukan gwamnatin da su fito su kwatanta abubuwan da gwamnatin Tinubu ta cimma a Abuja da na gwamnatocin da suka gabata.

“A tarihin FCT, babu wata gwamnati da ta yi abin da muka yi a Abuja. Ina kalubalantar duk wanda yake ganin akasin haka ya fito ya bayyana.” in ji shi.

Wike ya kuma soki taron kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) da aka gudanar kwanan nan, inda ya bayyana taron da kusan wasan yara. Ya zargi shugabancin kungiyar da bai wa siyasa muhimmanci fiye da batutuwan da suka shafi aikin lauya.

“Maimakon su mayar da hankali kan batutuwan da suka shafi NBA, sai suka fara siyasa.” in ji Wike.

Ya kuma yi tambaya kan abin da shugabar NBA ta yanzu za ta bari a matsayin abin tunawa bayan ta kammala wa’adinta, yana mai cewa ya taba bayyana dalilin da ya sa bai goyi bayan fitowarta a matsayin shugabar kungiyar ba.

Wike ya kara sukar matakin gayyatar wani tsohon gwamna zuwa taron NBA, duk da zargin da ya yi cewa tsohon gwamnan ya hana kotuna gudanar da ayyukansu na kusan shekaru biyu.

“Zan tambayi shugabar NBA: me za ki ce shi ne abin da za ki bari a baya a matsayin aikin da ki ka yi? Ni kuma a matsayina na Ministan FCT, me zan ce na yi?” in ji shi.

“Na shaida wa shugabar NBA ta yanzu dalilin da ya sa ban goyi bayanta ba. Ta je ta gayyaci wani tsohon gwamnan jihar da ya daure ya kuma kulle kotu na kusan shekaru biyu. Idan ka ga irin wannan abu, sai ka fara tambayar kanka, wace irin NBA ce wannan?”

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments