Saturday, October 17, 2026
HomeKasuwanciFarashin fetur ya ƙaru a gidajen mai da dama a Abuja

Farashin fetur ya ƙaru a gidajen mai da dama a Abuja

Gidajen mai da dama a Abuja sun ƙara farashin litar fetur, lamarin da ya sa masu ababen hawa ke biyan kuɗi fiye da yadda suke biya a baya.

Gidajen mai da dama a Abuja sun ƙara farashin litar fetur, lamarin da ya sa masu ababen hawa ke biyan kuɗi fiye da yadda suke biya a baya.

Ƙarin farashin ya zo ne bayan matatar man fetur ta Dangote ta ƙara farashin da take sayar da man ga dillalai daga N1,200 zuwa N1,265 kan lita ɗaya cikin makon da ya gabata.

Binciken NAN ya nuna cewa kamfanin AY Shafa ya ƙara farashin fetur daga N1,250 zuwa N1,270 kan lita, yayin da Optima ya tashi daga N1,260 zuwa N1,300. Haka kuma, NNPC ya ƙara farashinsa daga N1,250 zuwa N1,270.

Wani masanin tattalin arziki, Samson Ogunjimi, ya bayyana damuwa kan yadda hauhawar farashin man ke ƙara jefa ‘yan Najeriya cikin matsin tattalin arziki, inda ya yi kira ga gwamnati ta ɗauki matakan rage tasirin farashin ga jama’a.

A nasa ɓangaren, Kakakin IPMAN na ƙasa, Chinedu Ukadike, ya ce masu sayar da man sun tilasta yin gyaran farashi ne sakamakon sauye-sauyen farashin Dangote. Ya ce ba za su iya ci gaba da sayar da fetur ƙasa da kuɗin da za su kashe wajen sake cike hajarsu ba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments