Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ya kalubalanci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, kan alkawarinsa na sake buɗe iyakokin Najeriya idan ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Tunji-Ojo ya ce iyakokin Najeriya ba a rufe suke ba, don haka ba daidai ba ne a ce za a “sake buɗe” su.
Ministan ya bayyana cewa gwamnatin Najeriya na ci gaba da ba da damar zirga-zirga da kasuwanci ta kan iyakokin ƙasar, yayin da Hukumar Kula da Shige da Fice ke kula da harkokin shige da fice da tsaron iyakokin.
Ya kuma bayyana cewa an sake buɗe wasu manyan mashigar kan iyaka a baya, ciki har da Seme, Illela, Maigatari da Mfum, sannan daga bisani aka sake buɗe wasu kamar Idiroko da Ikom.
Tunji-Ojo ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kuma sake buɗe Kamba da Tsamiya a Jihar Kebbi a watan Fabrairun 2026.
Sai dai ministan ya amince cewa wasu mashigar kan iyaka, musamman a arewacin Najeriya, ba sa aiki yadda ya kamata saboda matsalolin tsaro.
Ya ce ba za a iya buɗe irin waɗannan wurare ba tare da tabbatar da tsaron mazauna yankunan da ’yan kasuwa ba.
Tunji-Ojo ya bukaci Atiku da ya yi cikakken bayani kan sabon tsarin da yake son amfani da shi wajen kula da iyakokin Najeriya idan ya zama shugaban ƙasa, maimakon kawai yin alkawarin sake buɗe su.