Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ya bukaci Ƙungiyar Daliban Najeriya (NANS) da sauran shugabannin ɗalibai su yi ƙoƙarin tattara kuri’u miliyan 10 domin bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu goyon baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Ministan ya yi wannan kira ne a Abuja yayin da ya karɓi bakuncin shugabannin NANS da wasu ƙungiyoyin ɗalibai da suka kai masa ziyara.
A cewar Alausa, ci gaba da mulkin Tinubu zai taimaka wajen dorewar wasu daga cikin sauye-sauyen da gwamnatin ke aiwatarwa a fannin ilimi.
Ya ambaci tallafin ɗalibai, koyar da sana’o’i, gina da gyaran makarantu da kuma faɗaɗa damar samun ilimin gaba da sakandare a matsayin wasu daga cikin abubuwan da gwamnati ke mayar da hankali a kai.
Ministan ya kuma bayyana Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Najeriya (NELFUND) a matsayin ɗaya daga cikin manyan shirye-shiryen gwamnatin Tinubu, inda ya ce an ware kusan Naira biliyan 200, yayin da sama da ɗalibai miliyan 1.6 suka amfana da shirin.
Ya ƙara da cewa gwamnati na zuba jari wajen gina ɗakunan kwanan ɗalibai, ilimin fasaha da sana’o’i (TVET), sufuri a jami’o’i, makamashin sabuntawa da kuma tallafa wa harkokin kasuwancin ɗalibai.
A nasa ɓangaren, Shugaban NANS, Babatunde Afeez Akinteye, ya yaba da wasu shirye-shiryen gwamnati, sai dai ya buƙaci a magance matsalolin tallafin karatu na tarayya, karɓar ɗalibai ba bisa ƙa’ida ba da kuma matsalolin amincewa da wasu kwasa-kwasai.
Alausa ya tabbatar wa shugabannin ɗaliban cewa ma’aikatar za ta duba korafe-korafensu tare da ƙara ƙarfafa tsarin karɓar ɗalibai, domin tabbatar da cewa ba a shigar da su cikin shirye-shiryen da hukumomin da suka dace ba su amince da su ba.