Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, Atiku Abubakar, ya ce zai sake buɗe iyakokin Najeriya da ƙasashen maƙwabta idan ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Atiku ya bayyana cewa rufe iyakokin ya yi mummunar illa ga tattalin arzikin ƙasar, musamman a jihohin Arewa da ke da iyaka da Kamaru, Chadi, Nijar da Jamhuriyar Benin.
A cewarsa, matasa da dama da ke dogaro da cinikin ƙetare sun shiga cikin matsanancin hali, yayin da wasu ’yan kasuwa suka durƙushe sakamakon takunkumin da aka sanya kan harkokin kasuwanci ta kan iyakoki.
Ya ce sake buɗe iyakokin zai taimaka wajen farfaɗo da cinikin ƙetare, samar da ayyukan yi da kuma dawo da hanyoyin samun kuɗin shiga ga al’ummomin da ke zaune a yankunan kan iyaka.
Atiku ya ce manufarsa ita ce samar da tsarin da zai ba da damar gudanar da halastaccen ciniki tsakanin Najeriya da ƙasashen maƙwabta, tare da kare muradun tattalin arzikin ƙasa.