Saturday, October 17, 2026
HomeKasashen wajeTsananin zafi ya yi sanadin mutuwar mutane 15,800 a Jamus

Tsananin zafi ya yi sanadin mutuwar mutane 15,800 a Jamus

Akalla mutane 15,800 ne aka kiyasta cewa sun rasa rayukansu a Jamus sakamakon tsananin zafi a wannan bazarar, a cewar sabon rahoton Cibiyar Kiwon Lafiyar Jama’a ta Robert Koch Institute.

Rahoton ya nuna cewa mutanen da suka fi fuskantar barazanar mutuwa sakamakon zafin sun hada da wadanda shekarunsu suka haura 75.

A wani mako guda a karshen watan Yuni, an kiyasta mutuwar mutane kusan 9,600 sakamakon tsananin zafi, lokacin da yanayin zafi a wasu sassan kasar ya haura digiri 40 a ma’aunin Celsius.

Haka kuma, an samu wasu mutuwar da suka danganci zafi tsakanin karshen Yuli zuwa tsakiyar watan Agusta.

RKI ta ce wannan shi ne adadin mutuwar da ta yi sanadin zafi mafi yawa cikin shekaru goma da suka gabata, inda adadin da ya fi kusa da wannan shi ne na shekarar 2018, lokacin da aka kiyasta mutuwar mutane kusan 8,900.

Masana sun ce tsananin zafi na iya haddasa mutuwa kai tsaye, amma kuma yana iya kara tsananta wasu cututtuka da suka shafi zuciya, huhu da koda, musamman ga tsofaffi.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments