Saturday, October 17, 2026
HomeSiyasaAtiku ya mayar wa Tinubu martani kan batun tallafin man fetur

Atiku ya mayar wa Tinubu martani kan batun tallafin man fetur

Dan takarar shugaban kasa na ADC a 2027, Atiku Abubakar, ya ce shirin da ya gabatar na tallafa wa fannin man fetur ba wai nufinsa shi ne dawo da tsohon tsarin tallafin mai ba.

Atiku ya ce yana son samar da wani tsari na wucin gadi kuma mai iyaka, wanda zai karfafa samar da man fetur a cikin gida tare da rage wa ‘yan Najeriya radadin tashin farashin mai.

Ya ce tsarin zai kasance karkashin kasafi da sa ido mai tsauri domin tabbatar da cewa an yi amfani da kudaden yadda ya kamata.

Atiku ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da kara tsananta matsin tattalin arziki tun bayan cire tallafin man fetur, yana mai cewa farashin mai, sufuri da kayan abinci sun tashi, yayin da darajar Naira ta ragu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments