Bankin Duniya ya bayyana wani sabon tsarin hadin gwiwa da Najeriya na shekarar 2026 zuwa 2032, wanda ke da burin kara yawan ‘yan Najeriya da ke samun wutar lantarki da kuma inganta wasu muhimman bangarorin tattalin arziki.
A karkashin tsarin, ana sa ran samar wa mutane miliyan 32 damar samun wutar lantarki, yayin da karin mutane miliyan 58 za su samu damar amfani da intanet.
Bankin ya kuma tsara tallafa wa manoma miliyan 9.5 domin inganta noma, kara darajar amfanin gona da kuma taimaka musu wajen samun kasuwannin da za su sayar da amfanin gonarsu.
Haka kuma, Bankin Duniya na sa ran jawo jarin masu zaman kansu da ya kai dala biliyan 4.1 domin bunkasa ababen more rayuwa da wasu muhimman sassa na tattalin arzikin Najeriya.
Mukaddashin Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Taimur Samad, ne ya gabatar da sabon tsarin hadin gwiwar a Legas.
Shirin ya kuma kunshi tallafawa kanana da matsakaitan sana’o’i, samar da ayyukan yi, inganta kiwon lafiya da ilimi, da kuma shirye-shiryen taimaka wa al’umma wajen tinkarar sauyin yanayi.
A bangaren ilimi, ana sa ran dalibai miliyan 19.4 za su amfana da shirye-shiryen inganta ilimi, yayin da mutane miliyan 40 za su amfana da wasu shirye-shiryen kiwon lafiya da abinci mai gina jiki.
Bankin ya ce manufar tsarin ita ce taimakawa Najeriya wajen samar da ci gaba mai dorewa, bunkasa tattalin arziki da kuma inganta rayuwar miliyoyin ‘yan kasar.