Sunday, October 18, 2026
HomeSiyasaSiyasar Shekarau, Ganduje da Abba ta zo karshe a Kano – Kwankwaso

Siyasar Shekarau, Ganduje da Abba ta zo karshe a Kano – Kwankwaso

Mataimakin ɗan takarar jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce tsofaffin gwamnonin Kano, Ibrahim Shekarau da Abdullahi Ganduje, da kuma Gwamna Abba Kabir Yusuf, sun rasa ƙarfin siyasa a jihar.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wata hira da NAN a Abuja, inda ya ce siyasar da aka gina bisa “cin amana” ba ta daɗewa.

Game da Ganduje, Kwankwaso ya ce rikicinsu ya fara ne bayan tsohon gwamnan ya fara ƙalubalantar tsarin siyasar da suka gina tare, lamarin da ya ce ya yi sanadin koma bayan siyasarsa.

Dangane da Gwamna Abba Kabir Yusuf kuwa, Kwankwaso ya ce shi da magoya bayansa sun yi ƙoƙari wajen ganin Abba ya samu nasara a zaɓen 2023, amma daga baya gwamnan ya nisanta kansa daga ƙungiyar siyasar da ta taimaka wajen ɗora shi kan mulki.

Ya kuma zargi Abba da ƙoƙarin maye gurbinsa a matsayin jagoran siyasar Kano, yana mai cewa lokaci ne zai tabbatar da sakamakon irin waɗannan matakai.

Kwankwaso ya ƙara da cewa sauyin alaƙa tsakanin ’yan siyasa da tsoffin abokan hulɗarsu ba sabon abu ba ne a Najeriya, sai dai ya ce abin da ya faru a Kano ya fi fice.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments