Jam’iyyar APC a Jihar Osun ta ce shugabanninta na nazarin sakamakon zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar, tare da duba matakin da za ta ɗauka na gaba.
Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na jam’iyyar, Kola Olabisi, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a Osogbo.
APC ta ce za ta yi amfani da dukkan hanyoyin da kundin tsarin mulki da dokar zaɓe suka tanada domin kalubalantar duk wani abu da ta ga bai dace ba.
Jam’iyyar ta buƙaci magoya bayanta su kasance cikin nutsuwa, su ci gaba da harkokinsu tare da guje wa duk wani abu da zai iya haifar da rikici.
Ta kuma ce za ta tuntubi lauyoyinta domin samun shawarar doka kan matakin da ya dace ta ɗauka, tana mai cewa “ba a gama ba har sai an gama.”
Hukumar INEC ta ayyana Gwamna Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya samu 511,067 na ƙuri’u, yayin da ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, ya samu 444,815.
Dan takarar ADC, Najeem Salaam, ya zo na uku da ƙuri’u 17,180.