Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiNajeriya da Saudiyya sun kulla yarjejeniyar inganta tsaro

Najeriya da Saudiyya sun kulla yarjejeniyar inganta tsaro

Najeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna ta shekaru biyar, don karfafa hadin gwiwar tsaro a tsakanin kasashen biyu.

A cikin wata ranar sanarwar da Ahmed Dan Wudil, Mataimaki na Musamman kan yada labarai ga karamin Ministan tsaro, Bello Matawalle, ya fitar, ta bayyana cewa, hadin gwiwar ta shafi dabarun horar da sojoji, raba bayanan sirri, samar da tsaro, da ayyukan hadin gwiwa.

An sanya hannu a yarjejeniyar ne a Birnin Riyadh na kasar Saudiya, ta hannun karamin Ministan tsaro na, Bello Matawalle, da Dr. Khaleed Al-Biyari na Saudiyya, wacce ake sa ran yarjejeniyar za ta zama tsarin ci gaban tsaro mai dorewa a fadin kasashen biyu.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments