Rundunar sojin Najeriya ta takwas ta ce dakaru na musamman na Operation Fansan Yamma da aka tura daƙile aika-aikar ‘yan fashin daji da ta’addanci a jihar Sokoto sun yi wa ɓarayin daji wani kwanton-ɓauna inda suka kashe 11 tare da ƙwace tarin makamai.
Wata sanarwa da rundunar sojin ta wallafa a shafinta na X ta ce dakarun sun cimma wannan nasara ne ta hanyar wani farmakin dabara a ƙauyen Kurawa da ke ƙaramar hukumar Sabon Birni inda suka daƙile wani hari da ‘yan bindiga suka yi shirin kai wa a ƙauyen Tara.
Sanarwar ta ce dakarun sun yi aiki ne da bayanan sirri wajen aiwatar da kwanton-ɓaunar inda suka yi bata-kashi da ‘yan bindigan kafin su ci ƙarfinsu.