Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiDole a binciki kisan mata 9 da sojoji suka yi a Adamawa...

Dole a binciki kisan mata 9 da sojoji suka yi a Adamawa – Amnesty International

Amnesty International ta bayyana cewa dole ne a binciki kisan wasu mata 9 da sojoji suka yi a yayin zanga-zanga a Adamawa

Kungiyar kare hakkin ɗan’adam ta Amnesty International ta bukaci hukumomin Najeriya su gudanar da cikakken bincike kan zargin amfani da karfin da ya wuce kima da sojoji suka yi, wanda ake zargin ya yi sanadin mutuwar aƙalla mata tara a yayin zanga-zanga a Karamar Hukumar Lamorde ta jihar Adamawa.

Hakan dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a shafin ta na sada zumunta Facebook.

Ƙungiyar ta ce harbin da aka yi wa masu zanga-zangar da harsasai kai tsaye ba tare da gargadi ba ya saɓa ƙa’ida kuma ba ya kan doka.

Rahotanni dai sun nuna cewa waɗanda suka jikkata sun samu harbin bindiga a sassan jikinsu daban-daban, ciki har da kai da wuya da baya da kirji da kafada da kafa da kuma hannuwa, wasu ma an harbe su sau da dama.

Amnesty International ta kara jaddada cewa akwai buƙatar ɗaukar mataki domin dakile rikicin kabilanci da ya ta’azzara tsakanin ƙabilun Bachama da Chobo, rikicin da ya samo asali daga taƙaddama kan fili da zargin satar babur.

Kungiyar ta ce rikicin ya haifar da munanan laifuka da kashe-kashen da ke ci gaba da faruwa a yankin, tare da bayyana cewa halin ko-in-kulan da hukumomin Najeriya suke nunawa ya kara dagula lamarin.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments