Saturday, October 17, 2026
HomeLabaraiSoyinka ya kalubalaci yawan jami'an tsaro da ke tare da Seyi Tinubu

Soyinka ya kalubalaci yawan jami’an tsaro da ke tare da Seyi Tinubu

Fittaccen marubucin nan, Wole Soyinka ya soki tare da nuna damuwa kan yawan jami’an tsaro da ke tare da ɗan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu.

Da yake jawabi a bikin lambar yabo da ake bai wa waɗande suke ƙoƙari a aikin jarida ta WSCIJ a Legas, Soyinka ya ce irin wannan yawan jami’an tsaro na nuna rashin daidaito a tsarin tsaro da kuma abubuwan da Najeriya ke fifitawa.

Ya bayyana cewa; “Yayin da nake fito wa daga otal ɗin da nake, sai na ga taron mutane, ni na ɗauka ma ana ɗaukar fim ne a filn otal din saboda yadda kusan duka rundunar tsaro suka mamaye filin otal ɗin da ke iIkoyi.”

“Sai kuma na ga cewa ba haka bane, ashe wai jami’an tsaro ne da ke kare ɗan shugaban ƙasa ciki har da jami’an SWAT masu bindigu da yawa, har kimanin 15,z’ zagaye a wurin.

Soyinka ya ce abin ya ba shi mamaki har sai da ya kira mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, domin tabbatar da cewe hukumomi ne suka ba shi yawan jami’an tsaro ko kuma hakan ya dace.

SourceBBc Hausa
RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisment -
Google search engine

Most Popular

Recent Comments